(ABNA24.com) - Wata majiyar ‘yansanda a lardin Asir na kasar Saudiya ta bayyana cewa mutane 6 sun rasa rayukansu a yayinda wasu 3 suka ji rauni sanadiyyar harbe-harbe a garin Al-Amwah na yankin.
Kamfanin dillancin labaran Spotnic na kasar Rasha ya kara da cewa labarin bai bayyana dalilan harbe-harben ba, sai dai jami’an tsaron kasar sun ce sun fara gudanar da bincike don tabbatar da abinda ya Faru.
Mallakar makamai a kasar Saudiya dai ya zama ruwan dare duk da cewa a hukumance ba wanda yake da izinin mallaar makamai in banda Jami’an tsaron kasar.
Yankin Asir dai yana kan iyakar kasar ta Saudiya da kasar Yemen ne, wacce take cikin yaki da kasar da Saudiya da kawayenta tun shekara ta 2015.
/129
28 Mayu 2020 - 05:07
Lambar labari: 1040855
Wata majiyar ‘yansanda a lardin Asir na kasar Saudiya ta bayyana cewa mutane 6 sun rasa rayukansu a yayinda wasu 3 suka ji rauni sanadiyyar harbe-harbe a garin Al-Amwah na yankin.